Spain: An kama masu coge a tennis

Tennis Match fixing

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cogen da ake zargi an yi, sun faru ne a Spain da Portugal, in ji hukumomi

'Yan sanda a Spain sun kama mutane 34 bisa zarginsu da hannu a wata kungiya ko gungun masu coge da magudi a wasan tennis a Spain din da kuma Portugal.

Wadanda aka kama sun hada da 'yan wasan tennis guda shida, kamar yadda ministan harkokin cikin gida na Spain din ya sanar ba tare da ya bayyana sunan kowa daga cikinsu ba.

Ana zarginsu ne da yin coge a wasannin tennis din da dama ta yadda ake doke su a wasan, kuma sun yi haka akalla a wasa 17 daban-daban.

Hukumomi sun ce kudin da mutanen suka samu daga magudin ya haura euro dubu 500 ( fan 420,420).

Kakakin 'yan sanda ya sheda wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ana ba wa 'yan wasa tsakanin euro 500 (fan 419) da euro 1,000 (£837) domin a cinye su a wasa.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce a wani lokacin ana yi musu alkawarin euro 500 amma daga karshe sai a ba sueuro 50 kawai.

Dukkanin 'yan wasan da lamarin ya shafa dai kusan kanana ne, ba sa cikin kwararru 800 na duniya.

Watan Janairu wani binciken hadin guiwa da BBC da Buzzfeed News suka gudanar ya gano tarin shedar coge a manyan wasannin tennis na duniya.

Bincikin ya gano hannun 'yan wasa 16 , wadanda suna cikin manyan 'yan wasa 50 a cikin shekara goma da ta wuce.

An yi ta gabatar da su ga hukumar tabbatar da da'a a wasan tennis a kan zargin shirya magudi a wasannin.

Amma duk da haka an kyale su, su cigaba da wasa, cikinsu har da wadanda suka ci manyan kofuna na wasannin tennis.