Boksin: Anthony Joshua ya dauki kocin Birtaniya

Anthony Joshua

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Anthony Joshua ya ce yana farin ciki Rob McCracken ya kasance tare da shi a wurin dambensa

Zakaran boksin ajin masu nauyi mai rike da kambun hukumar IBF, Anthony Joshua ya dauki darektan kula da kwazon tawagar 'yan damben boksin ta Birtaniya a matsayin kocinsa.

Dan damben na Birtaniya mai shekara, 27, zai kasance da darektan, Rob McCracken, a bangarensa a lokacin karawar kare kambunsa na IBF, da Eric Molina a Manchester ranar 10 ga watan Disamba.

Joshua ya ci lambar zinare ta damben boksin a gasar Olympics da aka yi a Landan a 2012 karkashin kulawar McCracken, kafin ya juye ya shiga damben boksin na kwararru a 2013.

McCracken, wanda zai ci gaba da rike mukamin nasa na darektan tawagar boksin din ta Birtaniya, bayan aikin horad da Joshuan, a da ya yi aiki da Carl Froch kafin ya yi murabus a bara.

Kocin da daman yake horad da Joshua, Tony Sims, zai cigaba da aiki da shi a matsayin mataimakin McCracken.

An ruwaito Joshua yana cewa, ''na rike alakata kut da kut da Rob da kuma tawagar boksin ta Birtaniya tun 2012.

Kodayaushe ina neman shawara daga wurinsa, saboda haka ina matukar farin ciki ya kasance a wurina a lokacin dambe."