Chelsea ta ci Man City 3-1 a Ettihad

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Chelsea ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Premier

Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Chelsea da ci 3-1 a gasar Premier wasan mako na 14 da suka fafata a ranar Asabar a Ettihad.

Manchester City ce ta fara cin kwallo, inda Gary Cahill ya ci gida, bayan da Jesus Navas ya bugo kwallo ta bugi kafarsa ta fada ragar Chelsea daf da za a je hutu.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Chelsea ta farke ta hannun Diego Costa kuma kwallo na 11 da ya ci a gasar Premier bana, sannan William da Hazard kowannensu ya ci guda-guda.

Manchester City ta karasa karawar da 'yan wasa tara a cikin fili, bayan da alkalin wasa Anthony Taylor ya kori Sergio Aguero da kuma Fernandinho daf da za a tashi daga wasan.

Da wannan sakamakon Chelsea ta ci wasannin Premier takwas a jere wanda rabon da ta yi hakan tun a kakar wasa ta 2010/2011.

Chelsea wadda ta ci gaba da zama a kan teburin Premier da maki 34, ta taba lashe wasanni tara a jere a gasar a kakar wasan 2006/07.