Super Falcons ta lashe kofin Afirka na bana

Super Falcons

Asalin hoton, Super Sport

Bayanan hoto,

Oparanozi ce ta ci kwallon da ya bai wa Nigeria damar lashe kofin Afirka na bana

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Super Falcons, ta lashe kofin nahiyar Afirka, bayan da ta doke ta Kamaru da ci 1-0 a karawar da suka yi a ranar Asabar a Kamaru.

Da wannan sakamakon Nigeria wadda ke rike da kofin, ta lashe karo na 10 jumulla a tarihi, inda ta fara daukar kofin farko a shekarar 1991.

Wannan ne karo na hudu da Nigeria ke cin Kamaru a wasan karshe a gasar kofin nahiyar Afirka ta Mata.

Nigeria ta fara cin kamaru a wasan karshe 2-0 a gasar farko a shekarar 1991 a Legas, sannan ta doke Kamaru 4-0 a wasa na biyu a shekarar a Yaounde.

Super Falcons ta kara doke Kamaru da ci 5-0 a wasan karshe a shekarar 2004, sannan ta kara samun nasara da ci 2-0 a wasan karshe a gasar da aka yi a 2014.

Nigeria ta dauki kofin a shekarar 1991, 1995, 1998, 2000, 2002, 2004, 2006, 2010 da kuma 2014, inda Equotorial Guine ta dauka sau biyu a shekarar 2008 da kuma 2012.

Za a buga gasar cin kofin kwallon kafa ta mata a shekarar 2018 a Ghana.