Barcelona da Real Madrid sun tashi 1-1

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid ta ci gaba da zama a kan teburin La Liga, inda Barcelona ke biye da ita

Barcelona da Real Madrid sun tashi wasa kunnen doki 1-1 a gasar La Liga wasan mako na 14 da suka fafata a ranar Asabar a Nou Camp.

Barcelona ce ta fara cin kwallo ta hannun Luis Suarez a karon battar da ake yi wa lakabi da El Clasico.

Madrid ta farke kwallon ne daf da za a tashi ta hannun Sergio Ramos, wanda hakan ya sa ta yi wasanni 33 a jere ba tare da an doke ta ba.

Rabon da a ci Madrid a wasa tun rashin nasara da ci 2-0 da ta yi a hannun Wolfsburg a wasan cin kofin zakarun Turai a ranar 6 ga watan Afirilun 2015.

Madrid din ta karasa wasannin bara guda goma ba a doke ta ba, yayin da ta buga fafatawa 22 a bana ba a samu nasarar doke ta ba.

Real Madrid ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburinb La Liga da maki 34, inda Barcelona ke matsayi na biyu da maki 28.