Arsenal ta caskara West Ham da ci 5-1

Asalin hoton, EPA
West Ham United ta koma mataki na 17 a kan teburin Premier da maki 12
Kungiyar Arsenal ta yi laga-laga da West Ham United inda ta doke ta da ci 5-1 a gasar Premier wasan mako na 14 da suka kara a ranar Asabar.
Arsenal ta ci kwallayenta ta hannun Mesut Ozil tun kafin a je hutu, bayan da aka dawo ne Alexis Sanchez ya ci uku rigis, sannan Oxlade-Chamberlain ya ci ta biyar a karawar.
Andy Carroll ne ya farke kwallo daya da West Ham ta ci a saura minti bakwai a tashi daga wasan na hamayya.
Da wannan sakamakon Arsenal wadda ta yi wasanni 14, ta dare mataki na biyu a kan teburi da maki 30, sai Liverpool ta uku wadda ta buga wasanni 13 da maki 30.