Dambe da aka yi tsakanin Mahaukacin Teacher da Garkuwan Alabo

Sa zare da aka yi tsakanin Aminu Mahaukacin Teacher daga Arewa da Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu a gidan damben Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja Nigeria a safiyar Lahadi.

Turmi biyu suka taka babu kisa, kuma tun kafin karawar sai da suka yi alkawarin cewar babu gudu ko ja da baya.