Bahagon Abba da Sisco sun buga canjaras

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

Bahagon Sisco da Abban Na Bacirawa sun buga turmi uku babu kisa

Kimanin dambe 11 aka yi da safiyar Lahadi a gidan damben gargajiya na Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja Nigeria.

Sai dai wasanni biyar ne aka yi kisa da ya hada da wanda Bahagon Dogon Minista daga Kudu ya buge Gurgun Arewa da wanda Shagon Bahagon Dan Kanawa daga Kudu ya samu nasara a kan Shagon AK daga Arewa.

Haka kuma Shagon Dan Sama'ila daga Kudu ya buge Bahagon Sunusi Dan Auta daga Arewa da wanda Shagon Habu Nasarawa daga Arewa ya buge Shagon Dan Digiri.

Wasa na biyar da aka yi kisa shi ne wanda Nokiyar Dogon Sani daga Arewa ya buge Dan Bahagon Mai Maciji daga Kudu.

Sauran wasannin da aka yi canjaras kuwa:

Shagon Bahagon Musa daga Arewa da Bahagon Dogon Auta daga Kudu

Bahagon Babangida daga Kudu da Shagon Buzu daga Arewa

Shagon Abba daga Arewa da Bahagon Sisco daga Kudu

Shagon Dan Digiri daga Kudu da Nura Dogon Sani daga Arewa

Shagon Shamsu daga Arewa da Na Balbali daga Kudu

Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu da Aminu Mahaukacin Teacher daga Arewa