Bounemouth ta doke Liverpool 4-3

Ryan Fraser

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ryan Fraser shi ne gwarzon Bournemouth bayan an dawo hutun rabin lokaci, kuma ya taimaka a kwallaye ukun farko da suka ci, ciki har da ta biyu da ya ci

Bournemouth ta doke Liverpool da ci 4 da 3 a gidanta a karon farko a wasan gasar Premier na mako na 14.

Sadio Mane ne ya fara ci wa bakin a minti na 20 da shiga fili, kuma minti biyu tsakani Origi ya kara ta biyu.

A minti na 55 ne Bournemouth ta sako Ryan Fraser sai wasa ya sauya salo, inda 'yan dakikoki da shigarsa Milner ya doke shi alkalin wasa ya bayar da fanareti, kuma Wilson ya buga ya ci.

Can ya kara ci wa Liverpool kwallonta ta uku a minti na 64, amma kuma a minti na 76 Fraser ya farke wa masu masaukin bakin ta biyu.

Bayan wasu mintina biyu ne kuma sai Cook ya farke wa Bournemouth kwallo ta uku.

An shiga karin lokaci da minti uku, bayan minti 90 ne sai Ake ya ci wa Bournemouth kwallon ta hudu, wadda ta ba ta nasara ta samu maki 18 kuma ta zama ta 14 a tebur.

Ita kuwa Liverpool yanzu ta zama ta uku a tebur da maki 30, a bayan Arsenal mai maki 31, yayin da Chelsea ke matsayin ta daya da maki 34.