Premier: Everton ta yi 1-1 da Man United

Everton Fans watch Ibrahimovic's goal

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Magoya bayan Everton sun zuba ido su ga ko kwallon Ibrahimovic za ta ci ko ba za ta ci ba

Dan wasan baya na Manchester United Marouane Fellaini ya yi kasassabar da ta jawo musu fanareti a karawarsu da tsohuwar kungiyarsa Everton suka tashi 1-1 a Goodison Park.

A minti na 85 ne aka sako Fellaini wanda wannan shi ne wasansa na 100 a United, amma babban abin da za a ce ya yi a wasan da shigowarsa shi ne janyo fanareti bayan da ya gwabje Idrissa Gueye a cikin da'irarsu, inda Baines ya buga kuma ya ci a minti na 89.

Zlatan Ibrahimovic ne ya fara cin kwallon da ta sa Manchester United a gaba a minti na 42, da kwallonsa ta shida da ya ci a wasa biyar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ibrahimovic ya ci kwallo hudu a wasan Premier uku, bayan ya yi wasa shida bai ci kwallo ko daya ba a baya

Yanzu Everton ta zama ta takwas a teburin Premier da maki 20, yayin da Manchester United ke matsayi na shida da maki 21.

Kocin Manchester United ya dawo fili bayan hukuncin haramta masa zuwa bakin fili da aka yi na wasa daya, a makon da ya gabata.