El Clasico: Ramos ya kafa tarihi

Sergio Ramos equalizes for Real Madrid

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sergio Ramos ya ci kwallo a karawar hamayya ta El Clasico hudu

Kwallon da Sergio Ramos ya ci wa Real Madrid ya farke cin da Barcelona ta yi musu 1-1, a El Clasico ranar Asabar ita ce ta 75 da ya ci wa kungiya da kuma kasarsa.

Kwallon da ya ci a daidai karshen lokacin wasan ta sa ya zama dan wasan baya da ya fi cin kwallo, wanda yake buga wasa a wata babbar kungiya.

To amma duk da haka sai dai idan ya samu wani gagarumin cigaba, in ba haka ba, ba zai iya kawar da bajintar da ake da ita a tarihi ba.

Bajintar ita ce, ta tarihin da Kocin Everton Ronald Koeman, dan Barcelona a da, wanda ya ci wa kungiya da kasarsa kwallo 253.

Ciki har da kwallon da ta bakanta wa 'yan Ingila rai, wadda Koeman din ya ci daga bugun tazara a wasan da Holland ta ci Ingilan 2-0 na neman zuwa gasar kofin duniya ta 1994.

Ingila na neman ta ci wasan ta je gasar, kuma a dalilin rashin nasarar ba ta samu damar zuwa gasar ba.

Ronald Koeman, kanin tsohon kocin Feyenoord Erwin Koeman ne kuma dan tsohon dan wasan Holland Martin Koeman ne.