Premier: Kungiyar da ta fi sauya jerin 'yan wasa

Manchester City and Chelsea players brawling

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Manchester City biyu aka kora a wasan da Chelsea ta ci su 3-1 a Etihad

Chelsea ta yi canji takwas ne kawai a jerin 'yan wasan da ta saba fitowa da su a gasar ta Premier a bana, daga wasa zuwa wasa, wanda na baya-bayan nan shi ne wanda Cesc Fabregas ya maye gurbin Nemanja Matic a ranar Asabar.

A daidai wannan lokacin na gasar ta Premier Burnley ce kawai ta yi canjin da ba shi da yawa, inda a 2010, ta sauya 'yan wasa biyar daga wadanda ta saba amfani da su, a wasanninta 14 na farko.

Duk da wannan sauyi da suka yi sun yi kasa a teburin gasar a lokacin, amma ita Chelsea da a yanzu ta yi hakan ba ta koma baya ba, sai ci gaba ta yi.

Canje-canjen da Chelsea ta yi guda takwas:

Pedro ya canji Willian a wasa na 2

Willian ya canji Pedro a wasa na 3

Luiz ya canji Terry a wasa na 5

Fabregas ya canji Oscar a wasa na 6

Alonso ya canji Ivanovic a wasa na 7

Moses ya canji Fabregas a wasa na 7

Pedro ya canji Willian a wasa na 8

Fabregas ya canji Matic a wasa 14

A daya bangaren abokiyar karawar Chelsea, wato Manchester City, ta fi duk wata kungiya canza jerin 'yan wasanta a bana, inda ta yi sauyi sau 16.

Wannan ya sa suka zama kungiyoyi biyu da suke matsayi na 16 da suka fi yin wannan sauyi na 'yan wasansu bayan wasanni 14 a tarihin Premier.

Abokiyar hamayyarta Manchester United ta yi canji a jerin 'yan wasan da ta saba fitowa da su, sau 64 a 2001, abin da ya sa ta zama ta biyu da ta uku, da ta fi yin canjin.

Cesc Fabregas ya canza Nemanja Matic ranar Asabar, bayan wasanni biyar a jere ba tare da Chelsean ta yi sauyi ba.