An haramta wa Aguero wasa hudu

Sergio Aguero receives red card

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alkalin wasa ya kori Sergio Aguero saboda ketar da ya yi wa David Luiz

An haramta wa dan wasan Manchester City Sergio Aguero wasanni hudu bayan katin korar da alkalin wasa ya ba shi a wasan da Chelsea ta ci su 3-1 ranar Asabar a Etihad.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta tabbatar da hukuncin, sakamakon jan katin da aka ba shi.

Alkalin ya kori Aguero ne saboda yadda ya yi wa David Luiz keta lamarin da ya tayar da hatsaniya tsakanin 'yan wasan kungiyoyin biyu a kusan karshen wasan.

Tun a farkon wannan kakar an yi wa dan wasan na Argentina hukuncin haramcin wasanni uku saboda gula da ya yi wa Winston Reid na West Ham.

Wannan hukuncin ba zai yi wa kocinsu Pep Guardiola dadi ba, a burinsa na daukar kofin Premier.

Haka shi ma abokin wasan Agueron Fernandinho alkalin wasa ya kore shi a lokacin saboda yadda ya hambare Cesc Fabregas a wuya a yayin hatsaniyar.

Shi ma dan wasan na tsakiya na Brazil za a haramta masa wasanni uku, kamar yadda bayanai suka nuna a shafin intanet na hukumar kwallon kafa ta Ingila.

Duk da wannan hukunci kocinsu Pep Guardiola ya ce Aguero zai iya buga musu wasan kofin zakarun Turai da za su yi da Celtic, ranar Talata.

Tuni Manchester City ta yi nasarar tsallakewa zuwa zagaye na gaba na 'yan 16, na sili-daya-kwale.