Blatter ya yi rashin nasara a kotu

Sepp Blatter

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Blatter ya ce ya karbi hukuncin, domin ba ya tsammanin wani na daban kuma

An jaddada hukuncin haramcin shiga harkokin wasanni na tsawon shekara shida da aka yanke wa tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, Sepp Blatter.

Kotun sauraron kararraki ta wasanni ce ta kara tabbatar da hukuncion bayan daukaka karar da Blatter mai shekara 80, ya yi a gabanta.

An yi wa Blatter dan Switzerland hukuncin ne bisa laifukan saba ka'idojin Fifa, kan yadda shugabancin nasa na hukumar na shekara 17 ya kare da badakalar cin hanci da rashawa a 2015.

An same shi ne da laifin biyan fan miliyan daya da dubu 300 ga tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Uefa, Michel Platini, abin da dukkaninsu suka ce ba su saba wata ka'ida ba.

Kotun sauraron kararrakin harkokin wasannin ta duniya ta bayyana biyan kudin,a matsayin tukucin da bai dace ba, wanda kuma ba shi da wani tshe ko dalili a kwantiragi.

Blatter ya ce, yanzu ba shi da ta cewa, ya karbi wannan hukunci, ya kara da cewa ya koyi abubuwa da dama a shekara 41 da ya yi a Fifa.

Kuma ya koyi sanin muhimmancin karbar kaddara musamman a wasa inda za ka iya yin nasara za kuma ka iya rashin nasara.

A watan Disamba na shekarar da ta wuce Fifa ta haramta wa Blatter da tsohon dan wasan Faransan Michel Platini shiga harkokin wasa tsawon shekara takwas, amma sauraren daukaka kara na hukumar ya rage hukuncin zuwa shekara 6.

Sannan kuma a watan Mayu kotun sauraron kararrakin wasanni ta duniya ta rage hukuncin Platini mai shekara 61 zuwa shekara hudu, bayan ya daukaka kara.

Dukkanin mutanen biyu sun ce kudin da kae zarginsu da yin almundahanar, kudi ne da shi Blattern ya biya Platini kan wani aiki na bayar da shawara da ya yi wa Blattern tsakanin 1998 da 2002.

Masu gabatar da kara na Switzerland ma na bincike kan biyan kudin.