Wasannin Zakarun Turai na Talata

Uefa Champions League Cup

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

A wasannin na Talata za a samu kungiyoyin da za su je zagayen 'yan 16 na gasar

A ranar Talatar nan za a ci gaba da wasu daga cikin wasannin karshe na ruku-rukuni na gasar cin kofin Zakarun Turai na Uefa, inda za a yi karawa takwas.

Daga cikin wasannin a rukuni na farko (Group A)Arsenal za ta je gidan FC Basel, yayin da PSG take gida da Ludogrets.

Sai rukuni na biyu (Group B) Dynamo Kiev tana gida Besiktas za ta same ta.

A rukuni na uku (Group C) Barcelona a gidanta za ta hadu da Borussia M' Glad Bach, ita kuma Mancity a Etihad za ta kara da Celtic.

A rukuni na hudu (Group D), Bayern Munich za ta karbi bakuncin Atletico Madrid, PSV Eindhoven ita ma tana gida da FC Rostov.

A wasannin Arsenal ta riga ta tsallake zuwa matakin 'yan 16 na sili daya kwale, kuma za ta kammala a matsayi na biyu a rukuninsu, idan PSG ta ci Ludogrets.

Ludogrets din kuma ita da FC Basel suna fafutukar samun gurbin zuwa gasar kofin zakarun Turai na Europa.

A wasannin Porto da Real Madrid da Bayern Munich da Benfica za su yi wasan ne na Talata suna matsayi na biyu a rukunansu.

A rukunin Napoli da Benfica da Besiktas komai zai iya kasancewa tsakaninsu.

Barcelona ta yi gaba a rukuninta, amma Man City ta biyu za ta iya rashi idan Borussia M Glad Bach ta ci Barca 6-0, Celtic kuma ta ci Man City ba tare da Cityn ta jefa kwallo ko da daya ba.

Atletico Madrid ta riga ta kankane matsayi na daya a rukuninsu, duk yadda wasa ya kasance Bayern Munich ce ta biyu.