Premier: Swansea ta bata rawarta da tsalle

Fernando Llorente da 'yan wasan Swansea

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Fernando Llorente ya ci wa Swansea kwallo biyu a wasan

Swansea ta yi wasan da ya kasance daya daga cikin mafi kayatarwa a Premier, a haduwarta da Crystal Palace, inda ta ci 5-4, amma a wasanta na gaba sai ta kasa kai hari ko daya.

A mako daya ta ga farin tamaula, inda ta yi ta zura kwallo a raga, amma kuma a mako na gaba sai ta ga bakin tamaular, kamar an yi ruwa an dauke.

A wasan ta kasa kai ko da hari kwaya daya ballantana ma ta jefa kwallo a raga, inda Tottenham ta ci su 5-0.

A wasan Tottenham ta kai hari 15 amma Swansea ba ta kai ko da daya ba, kuma ko da bugun gefe (kwana) daya ba ta samu ba.

Sai dai Swansean ta kai hari daya kacal a wasan gaba daya, kuma ko da wannan din ma bai tayar da hankalin mai tsaron ragar Hugo Lloris ba.

Sau daya kawai a Premier aka taba samun bambanci mai yawa na kai hari a wasa tsakanin kungiyoyi, a wasan da Man City ta kai wa West Brom hari sau 16, ita kuma ba ta kai ko da daya ba.

Sun yi wasan ne ranar 21 ga watan Maris na shekarar da ta wuce ta 2015.

Sai kuma wasan da Chelsea ta kai wa Burnley hari 15, ita kuma ba ta kai ko da daya ba.

A duk wadannan wasanni Tottenham ta fi cin moriya, inda ta ci kwallaye biyar, yayin da su kuwa Man City da Chelsea kowacce a nata wasan ta ci uku ba ko daya.