'Yan wasan Najeriya mata na yajin aiki

Wannan ba shi ne karon farko da Super Falcons ke samun matsala da NFF a kan kudinsu ba
'Yan wasan kwallon kafa mata na Najeriya Super Falcons sun yi zaman dirshan a otal din da suke a Abuja, sai an biya su hakkokinsu da alawus dinsu na cin kofin da suka yi.
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta yi wa zakarun na Afirka da suka dauki kofin kasashen Afirka a karo na takwas bayan sun ci Kamaru mai masaukin baki 1-0 ranar Asabar, alkawarin biyansu bashin kudaden da suke bi na baya kafin a fara gasar a Kamaru.
Wasu rahotanni sun bayyana hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta fitar da wata sanarwar inda ta ce babban sakatarenta Dakta Mohammed Sanusi, ya je otal din 'yan wasan inda ya gana da su da jami'ansu.
Sanarwar ta ruwaito Dakta Sanusin ya tabbatar da cewa 'yan wasan da jami'ansu suna bin kudaden, kuma ya ce ba sa farin ciki da hakan.
Amma saboda matsalar tattalin arziki da kasar ke ciki, za su ci gaba da rarrashin 'yan wasan da duk wadanda suke binsu kudade har lamarin ya inganta.
Duk da rokon da hukumar kwallon kafar ta Najeriya ta yi wa 'yan wasan su yi hakuri har al'amura su inganta, 'yan wasan na Super Falcons sun lashi takobin ci gaba da zaman dirshan din a otal.
Wannan ba shi ne karon farko da ake samun matsala tsakanin 'yan wasan mata na Najeriya da hukumar kwallon ta Najeriya, NFF ba a kan kudade.
Shekara 12 da ta wuce, 'yan wasan sun ki fita daga otal dinsu a Afirka ta Kudu har kwana uku, bayan da NFF din ta kasa biyansu kudadensu bayan sun ci kofin Afirkan na 2004.