Tennis: Djokovic ya raba gari da kocinsa

Djokovic da Boris Becker

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Djokovic ya fara aiki da Becker a watan Disamba na 2013

Zakaran wasan tennis na duniya sau goma sha biyu Novak Djokovic ya raba gari da kocinsa Boris Becker.

Djokovic ya yi aiki da tsohon zakaran gasar Wimbledon da gasar Amurka da ta Australia (US, Australian Open), har tsawon shekara uku.

Dan wasan na Serbia wanda shi ne na biyu a gwanayen tennis na duniya ya ci manyan kofuna shida a karkashin Becker.

Haka kuma ya rike dukkanin manyan kofuna na duniya hudu a lokaci daya, lokacin da ya ci kofin gasar Faransa a watan Yuni.

Da yake bayar da bayani kan rabuwar tasu, Djokovic ya ce, "burin da muka tsara za mu cimma lokacin da muka fara aiki tare mun cika shi gaba daya.

Saboda haka ina son in gode masa saboda hadin kai da aiki tare da sadaukar da kai da ya yi.''