Zakarun Turai: An yi tankade da reraya

Asalin hoton, EPA
Lucas Perez ya ci wa Arsenal kwallo biyu kafin ya ci mata uku a wasan Basel
A daren Talata ne aka kammala wasu daga cikin wasannin cin kofin zakarun Turai na rukuni-rukuni, guda 8, inda aka samu kungiyoyi 8 da suka shiga zagayen 'yan 16 na sili-daya-kwale.
Daga cikin wasannin a rukuni na farko (Group A)Arsenal ta je gidan FC Basel, ta lallasa ta 4-1, yayin da PSG a gidanta ta yi canjaras 2-2 da Ludogrets.
Sai rukuni na biyu (Group B) Dynamo Kiev a gidanta ta casa Besiktas 6-0.
A rukuni na uku (Group C) Barcelona a gidanta ta doke Borussia M' Glad Bach 4-0, ita kuwa Manchester city a Etihad ta yi 1-1 da Celtic.
A rukuni na hudu (Group D), Bayern Munich da ta karbi bakuncin Atletico Madrid ta ci bakin 1-0, PSV Eindhoven a gidanta ta yi canjaras 0-0 da FC Rostov.
Arsenal ta kai matakin 'yan 16, a matsayin ta daya a rukuninsu na farko (Group A) sakamakon nasarar da ta samu da maki 14.
Amma kuma kasancewar PSG ta tashi 1-1 da Ludogrets, abin da ya sa zakarun Faransan suka kammala a na biyu da maki 12 a rukunin.
Ludogrets din kuma da sakamakon da ta samu yanzu ta kawar da FC Basel a fafutukar samun gurbin zuwa gasar kofin zakarun Turai na Europa.
A rukunin na biyu (Group B) Napoli ta kammala a matsayi na daya da maki 11, yayin da Benfica ta zama ta biyu da maki 8.
Barcelona ita ce ta daya a rukuninsu na uku (Group C) da maki 15 yayin da Manchester City ta zama ta biyu da maki 9.
Atletico Madrid wadda daman ta riga ta kame matsayi na daya ta kammala da maki 15 a rukuni na 4 (Group D), Bayern Munich na bayanta da maki 12.
A ranar Laraba ne za a kammala sauran wasannin rukunan inda za a samu ragowar kungiyoyi takwas da za su cika 16 .
Ga wasannin:
Bayer Leverkusen da Monaco; Tottenham da CSKA Moscow; Real Madrid da Borussia Dortmund
Legia Warszawa da Sporting CP; Club Brugge da Kobenhavn; Porto da Leicester City
Lyon da Sevilla; Juventus da Dinamo Zagreb