Kofin Europa: Man Utd ta tafi Ukraine da 'yan wasa 19

Mourinho da 'yan wasan United
Bayanan hoto,

Man United na bukatar maki daya ne kawai ta je mataki na gaba na gasar ta Europa

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya tafi Ukraine da 'yan wasa 19 domin wasansu na karshe na rukuni na gasar Europa da Zorya Luhansk a ranar Alhamis.

Manchester United na bukatar maki daya ne kawai ta samu damar shiga mataki na gaba na gasar na sili-daya-kwale.

Michael Carrick da Matteo Darmian da Antonio Valencia da Memphis Depay da kuma Morgan Schneiderlin ba sa cikin 'yan wasan da aka yi tafiyar da su.

Shi kuwa Bastian Schweinsteiger bai cancanci yin wasa a gasar ba domin ba ya cikin tawagar 'yan wasan da tun da farko United din ta gabatar da sunayensu za su yi mata wasa a gasar ta Europa.

Chris Smalling da Luke Shaw su ma ba sa ciki domin har yanzu suna murmurewa daga raunukan da suka ji.

Ga tawagar 'yan wasan 19 : De Gea, Romero, Johnstone; Fosu-Mensah, Jones, Bailly, Rojo, Blind, Young; Fellaini, Herrera, Pogba, Lingard, Mata, Mkhitaryan; Martial, Rashford, Rooney, da kuma Ibrahimovic.