Lewandoski ya nuna matarsa na da juna biyu da kwallo

Robert Lewandoski

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Lewandoski ya ce, har kullum burinsa shi ne ya nuna wa duniya a filin kwallo matarsa ta samu juna biyu

Dan wasan gaba na Bayern Munich Robert Lewandoski ya yi amfani da wata hanya ta daban ya sheda wa duniya cewa matarsa ta samu juna biyu.

Dan wasan mai shekara 28 ya ci Atletico Madrid da bugun tazara, a wasan da suka tashi 1-0 na gasar cin Kofin Zakarun Turai na Uefa ranar Talata.

A yayin murnar cin kwallon, ya sanya babban dan yatsansa a baki, kamar yadda jarirai ke tsotson yatsa.

Sannan kuma ya daga rigarsa ya sanya kwallon, kamar mace mai juna biyu.

Hakan da ya yi ya nuna wa duniya ne cewa matarsa ta samu juna biyu, inda daga baya ya bayyana dalilin yin hakan.

Ya ce, ''A kodayaushe burina kenan na sanar a filin kwallo cewa matata ta samu juna biyu.''

''Kwallon da na ci na sadaukar da ita ga matata da jaririn da ke cikinta. Muna matukar farin ciki.''