'Na ji dadin cin kungiyata Man City'

Patrick Roberts lokacin da zai ci Man City Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Patrick Roberts ya ci wa Celtic kwallo 10 tun da ya koma a matsayin aro na wata 18 a watan Janairu, daga Man City

Dan wasan Celtic Patrick Roberts ya ce ya ji matukar dadin kwallon da ya ci Manchester City, kungiyar da ta bayar da shi aro, a wasan gasar Zakarun Turai.

Dan wasan mai shekara 19, wanda ya fara daga raga a wasan da suka tashi 1-1 ranar Talata, sau uku kawai Man City ta taba sa shi a wasa, kuma canji yake yi, tun da ya koma can daga Fulham.

Ya ce, ''daman an tsara yadda duk zai yi ya ci kwallon kuma komai ya tafi daidai, kuma ba shakka na ji dadinta sosai.

Domin ba a kodayaushe ba ne za ka iya cin kungiya irin wannan a gasar Zakarun Turai.

Na ji dadi matuka, saboda iyalai da 'yan uwana da yawa sun zo kallon wasan.

Wannan ne ya sa na zo Celtic domin in samu damar yin wasa irin wannan, samun damar wasa a gasar Zakarun Turai, shi ne babban burin.''

A kan dan wasan kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce: ''Dan wasa ne da zai bayar da mamaki a gaba. Na ji dadin yadda ya yi wasa.

Za mu tattauna a kan yadda za mu yi da shi a karshen kakar wasan bana.

Mun san irin matsayin kokarinsa, amma ba za mu yanke shawara a kan wasa daya ba. Abu ne na shekara daya.''