Roy Hodgson: Ina son komawa aikin koci

Roy Hodgson

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Roy Hodgson ya ce aikin koci ya zama kamar jininsa, ba zai iya rabuwa da shi ba

Tsohon kocin Ingila na kwallon kafa Roy Hodgson ya ce yana matukar sha'awar dawowa aikin koci, kuma yana ganin yanzu ma har sai ya fi da kokari.

Shi dai Hodgson ya bar aiki ne bayan da ba zato Iceland ta sha Ingila da mamaki inda ta fitar da ita da ci 2-1 a zagayen 'yan 16 na gasar cin kofin kasashen Turai ta 2016.

Sai dai kuma a karkashin jagorancinsa ne Ingila ta kafa tarihin zama ta biyar da ta taba zuwa gasar ta cin kofin Turai da nasarar cin dukkanin wasanninta dari bisa dari.

Tsohon kocin mai shekara 69 wanda ya ke da kwarewa ta aikin koci har tsawon shekara 40 ya ce " yana matukar sha'awar wasan kwallon kafa, wanda ya ma zama wani bangare na rayuwarsa.

Hodgson ya sheda wa BBC cewa, ''ina son shiga harkar kwallon kafa. Ina jin dadin haka. Idana aka neme ni da aikin koci, wanda na ga ya dace da ni, ba wata-wata zan karba.''

Hodgson ya ce ba ya fargabar wata takura da kalubalen aikin koci na yau da kullum. Ya ce idan ba na cikin harkar kwallon kafa ji nake kamar ban cika burina na rayuwa ba

Shi dai tsohon kocin tsawwon shekara hudu ya yi aikin horad da tawagar Ingila, bayan ya maye gurbin Fabio Capello dan Italiya, inda ya ci uku daga cikin wasanni 11 a wasannin manyan kofuna.

Tun lokacin da ya ajiye aiki, Ingila ta dauki Sam Allardyce wanda kuma ta raba gari da shi ta dauki Gareth Southgate bayan da ya yi aikin rikon kwarya na wasanni hudu.