Mourinho: Za mu yi wasa kamar a kan kankara

Zlatan Ibrahimovic

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ka san wanene wannan? Zlatan Ibrahimovic ne ya rufe kansa da fuska lokacin da suke atisaye cikin tsananin sanyi, mai kankara

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce da kamata ya yi a ce an yi wasansu na kofin Europa da Zorya tun farkon gasar saboda yadda filin yanzu ya zama kamar dutse saboda sanyi.

A yanzu daia an amince kungiyoyin su yi wasan a filin bayan da aka duba yanayin da yake a safiyar Alhamis.

Bayan da 'yan wasansa suka yi atisaye a filin ranar Laraba Mourinho ya ce filin yana da sanyi sosai, ya yi karau kamar dutse

Dole ne Manchester United ta tabbatar ba a doke ta ba a wasan domin ta kai zagaye na gaba na 'yan 32.

Ko da an ci United din, za ta wuce zuwa zagayen na gaba idan Feyenoord ta kasa cin jagora a rukuninsu Fenerbahce.

Ita dai kungiyar Zorya wadda Manchestern za ta kara da ita tuni an fitar da ita daga gasar.

United ta biyu a rukuni na daya (Group A), tana da tazarar maki biyu tsakaninta da Feyenoord ta uku, saboda haka ko da canjaras ta yi, za ta tsallake, ko da kuwa kungiyar ta Holland ta ci wasanta saboda, United tafi ta da yawan kwallaye.

Za a yi wasan na United na ranar Alhamis cikin tsananin sanyi kasa da da maki daya a ma'aunin Celcius

Mourinho ya ce: ''Ina ganin Uefa ta san yanayin filin kuma kowa ya san cewa a tsakiyar watan Disamba yanayin sanyi a Ukraine da Gabashin Turai yana da tsanani.''

"saboda haka idan da Uefa ta damu da hakan, da ta sauya lokacin wasannin yadda ba za a yi su ba a tsakiyar Disamba."