Dalung: NFF ce ta haddasa matsalar 'yan wasan Nigeria mata

Solomon Dalung
Bayanan hoto,

Dalung ya ce suna kokarin kawo karshen matsalar gaba daya

Ministan wasanni na Najeria Solomon Dalung ya ce zaman dirshan din da 'yan wasan Najeriya na kwallon kafa mata suke yi a otal kan kin biyansu kudadensu abin kaico ne, da NFF ta jawo.

'Yan wasan sun ci kofin kasashen Afirka na gasar kwallon kafar mata karo na takwas bayan sun doke Kamaru da ta karbi bakuncin gasar 1-0 ranar Asabar.

Bayan da suka dawo gida ne sai suka ki tafiya daga otal din da suke a Abuja, har sai gwamnati ta cika alkawarin da ta yi musu na ba wa kowace 'yar wasa dala 17,150 idan suka dauki kofin.

Ministan ya ce hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ce take da laifi a lamarin saboda ba ta mika bukatar bayar da kudin ba ga gwamnati a kan lokaci.

Barrister Dalung ya ce gwamnati na aiki tukuru domin shawo kan matsalar, kuma tana daukar matakin kawo karshen abin da ke haddasa irin wannan ki-kaka da sauran hukumomin wasanni.

Su dai 'yan wasan na Najeriya Super Falcons suna bin gwamnati kudaden alawus-alawus da sauran hakkokinsu na samun cancantar zuwa gasar da kuma na daukar kofin.

Wata daga cikin 'yan wasan ta gaya wa BBC cewa ba za su bar otal din Agura ba, inda aka sauke su har sai an ba wa kowacce daga cikinsu jumullar dala 23, 650.