Wenger: Za mu rike Sanchez da Ozil

Rex Features

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Kwallo 11 Sanchez ya ci a Premier bana Ozil kuma yana da hudu

Arsenal za ta yi duk abin da za ta iya domin ganin 'yan wasanta na gaba Alexis Sanchez da Mesut Ozil ba su bar kungiyar ba in ji kocinta Arsene Wengeri.

Ana rade radin 'yan wasan biyu za su koma wasu kungiyoyin, kasancewar saura wata 18 kwantiraginsu ya kare da Arsenal din kungiyar na tattaunawa da su kan sabuwar yarjejeniya.

Wenger ya ce: "wata 18 lokaci ne mai tsawo a harkar kwallon kafa. Wadannan 'yan wasan suna da sauran wata 18 months, za su kasance da mu tsawon wata 18, kuma muna fatan fiye da haka ma sosai.''

Ya kara da cewa: ''Bana jin wannan matsala ce.''

Da aka tambayi kocin ko zai saba ka'idar yadda kungiyar ke biyan 'yan wasa kudi, domin ganin 'yan wasa ba su tafi ba, sai ya ce, kamar koda yaushe za su yi duk abin da za su iya, kan kowane dan wasa.

A bana Sanchez dan kasar Chile ya ci wa Arsenal kwallo 11, kuma yana kan-kan-kan da Diego Costa a matsayin wadanda suka fi cin kwallo a Premier.

Wasu rahotanni na nuna cewa Chelsea da wata kungiyar China na son daukar dan wasan.