An dakatar da mai Leeds United wata 18

Massimo Cellino

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

A watan Afrilun 2014 Cellino ya mallaki Leeds United

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA ta dakatar da mai kungiyar Leeds United Massimo Cellino daga duk wasu harkokin wasa tsawon wata 18 da kuma cin tararsa fan 250,000.

Hukumar ta tuhume shi ne da laifin saba ka'idarta ta wakilin dan wasa a kan sayar da Ross McCormack ga kungiyar Fulham a 2014.

Haka kuma FA din ta ci tarar kungiyar ta Leeds United fan 250,000.

Cellino, wanda haramcin nasa zai fara daga ranar 1 ga watan Fabrairun 2017, tuni ya nuna aniyarsa ta daukaka kara kan hukuncin.

Kamar yadda sanarwar hukumar ta FA ta nuna, zuwa 30 ga watan Afrilu na 2017, Cellino zai halarci wani shiri na koyar da yadda aikin wadanda suka mallaki kungiyar kwallon kafa a Ingila da kuma darektoci yake, domin ya san kauli da ba'adin aikin.

Wannan shi ne karo na uku da FA ta ke dakatar da Cellino mai shekara 60, wanda shi ne da ya mallaki kungiyar Cagliari, tun lokacin da ya sayi kungiyar a Afrilun 2014.

Haka shi ma eja Derek Day hukumar ta kwallon kafar ta Ingila ta ci tararsa fan 75,000 kan rawar da ya taka wajen sayar da McCormack, shi ma kuma ta dakatar da shi wata 18.

Tun daga yanzu Derek Day zai yi hukuncin kaurace wa harkokin wasa na wata bakwai, sannan kuma sauran watannin 11 za a dage su har nan da shekara biyu, idan ya sake aikata laifi, sai a aiwatar da su.