Europa: Man United ta je zagaye na gaba

'Yan wasan Man United na murnar cin da Ibrahimovic ya yi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Man United za ta kasance cikin kungiyoyi 32 da ranar Litinin za a fitar da jadawalin yadda za su hadu a zagaye na gaba

Manchester United ta yi nasarar zuwa zagaye na gaba na 'yan 32 a gasar kofin Zakarun Turai na Europa bayan ta ci Zorya Luhansk 2-0.

Mkhitaryan ne ya fara ci wa United kwallonta a minti na 48 bayan an dawo daga hutun rabin lokaci sannan kuma Ibrahimovic ya kara ta biyu a minti na 88.

Da wannan nasara Manchester United ta gama wasannin na rukuni-rukuni a matsayin ta biyu a rukuninsu na farko, (Group A) da maki 12.

Ita kuwa Fenerbahçe wadda ta je gidan Feyenood ta ci ta 1-0, ta kasance ta daya a rukunin da maki 13, yayin da Feyenoord din ta yi waje da maki 7, ita ma Zorya Luhansk ta fita da maki 2.

Ita kuwa Southampton ta ga samu ta ga rashi, bayan da tana matsayi na biyu a rukuninta, Hapoel Beer Sheva ta Isra'ila ta kawar da ita, bayan da suka tashi wasa 1-1 a gidan 'yan Ingilan.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kungiyar Hapoel Beer Sheva ce kungiyar Isra'ila ta farko da ta taba nasara a Ingila

Kungiyar ta Hapoel Beer Sheva, wadda ba ta taba wasa a ainahin gasar Europa ba kafin bana, ta bi layin Manchester United da Tottenham a zagayen 'yan 32.

Ga kungiyoyin da suka yi nasarar zuwa zagayen 'yan 32 na daya da na biyu

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Group B Group c Group D Group E Group F

1 Apoel Nicosia 1, Saint-Étienne 1, Zenit St Petersburg 1, Roma 1,Athletic Bilbao

2 Olympiakos 2, RSC Anderlecht 2, AZ Alkmaar 2, Astra Giurgiu 2,KRC Genk

Group G Group H Group I Group J Group K

1, Ajax 1, Shaktar Donetsk 1, FC Schalke 04 1, Fiorentina 1, Sparta Prague

2, Standard Liege 2, KAA Gent 2, FK Krasnodar 2, PAOK Salonika 2, Hapoel Beer Sheva

Group L

1, Osmanlispor

2, Villarreal

A jadawalin da za a fitar ranar Litinin na wasan zagaye na biyu na 'kungiyoyi 32, Manchester United za ta iya haduwa da kowacce daga kungiyoyin da suka zo na daya a rukuninsu.

Ko kuma a hada ta da FC Copenhagen ko Lyon ko Besiktas, wadanda dukkaninsu sun fice daga gasar Zakarun Turai ta Uefa.