Fifa ta dakatar da wasu jami'an kwallon Afirka

Asalin hoton, Google
Bayan laifin rashawa Kirsten Nematandani ya kuma ki bayar da hadin kai wajen bincike
Fifa ta dakatar da tsohon shugaban hukumar kwallon kafar Afrika ta Kudu Kirsten Nematandani, daga shiga harkokin wasanni tsawon shekara biyar, saboda an same shi da laifin kin bayyana almundahana da kuma kin bayar da hadin kai ga bincike.
Laifin ya danganci wasu wasannin sada zumunta ne guda uku na kasa da kasa da aka yi a Afrika ta Kudu kafin gasar cin kofin duniya ta 2010.
A binciken da aka yi an gano cewa wata kungiyar 'yan caca ta Gabas mai Nisa ta shirya coge a wasannin.
Haka kuma FIfa ta haramta wa wani tsohon jami'in hukumar kwallon Zimbabwe Jonathan Musavengana, da tsohon kocin Togo Banna Tchanile, shiga harkokin wasanni tsawon rayuwarsu sakamakon laifin cin hanci da rashawa.
Mista Musavengana yana da hannu ne a wata cuwa-cuwa da aka biya 'yan wasan kasar Zimbabwe kudi domin su bari a ci su, a wasanni a yayin wani rangadi na Asia a 2009.
Shi kuwa Mista Tchanile an haramta ma sa shiga harkokin wasannin ne bayan da ya jagoranci wata tawagar 'yan wasan kasar Togo ta bogi zuwa Bahrain a 2010, inda aka ci 'yan wasan na bogi tarin kwallaye.