Arsenal ta hau kan teburin Premier

Premier

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Arsenal ta hada maki 34 iri daya da wanda Chelsea keda shi

Arsenal ta koma mataki na daya a kan teburin Premier, bayan da ta doke Stoke City 3-1 a gasar Premier wasan mako na 15 da suka kara a Emirates a ranar Asabar.

Stoke ce ta fara cin kwallo a bugun fenariti, bayan da Granit Xhaka na Arsenal ya yi wa Joe Allen na Stoke City gula a cikin da'ira ta 18.

Theo Walcott ne ya farkewa Arsenal daf da za a je hutun rabin lokaci, kuma kwallo na 100 da ya ci wa kungiyar tun komawarsa Gunners da murza-leda.

Mesut Ozil ne ya kara ta biyu a ragar Stoke daga baya kuma Alex Iwobi wanda ya shiga wasan a matsayin sauyi ya ci ta uku.

Arsenal din ta hada maki 34 iri daya da na Chelsea wadda za ta kara da West Brom a ranar Lahadi, Arsenal ta dara Chelsea da yawan cin kwallaye a raga.