Vardy ya ci mutuncin Manchester City

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasanni 16 Vardy ya yi wa Leicester City bai ci kwallo a raga ba

Jarmie Vardy ya kunyata Manchester City, bayan da ya zura mata kwallaye uku rigis a karawar da Leicester City ta ci Manchester City 4-2 a gasar Premier a ranar Asabar.

Leicester ta fara cin kwallo ne ta hannun Jarmie Vardy minti uku da fara wasa, kuma minti biyu tsakani King ya ci ta biyu.

A minti na 20 ne Vardy ya ci kwallo na uku kuma ta biyu da ya ci, daga baya ya kara ta hudu kuma ta uku da ya zura a ragar City saura minti 12 a tashi daga fafatawar.

Rabon da Vardy ya ci wa Leicester kwallo tun wasan da ta ci Liverpool 4-1 a ranar 10 ga watan Satumba, ya kuma yi wasanni 16 bai daga raga ba, sai a karawa da City nan da ya yi.

Saura minti takwas ya rage a tashi daga wasan City ta zare kwallo daya ta hannun Kolarov da kuma wadda Nolito ya ci daf da za a tashi daga gumurzun.

Leicester za ta buga wasan mako na 16 da Bournemouth. Yayin da Manchester City za ta kara ne da Watford.