Madrid ta kafa tarihin wasanni 35 ba a doke ta ba

La Liga

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Murnar kwallo na uku da Sergio Ramos ya ci wa Real Madrid

Real Madrid ta kafa tarihin buga wasanni 35 a jere ba a doke ta ba, bayan da ta ci Deportivo La Coruna 3-2 a gasar La Liga da suka kara a ranar Asabar.

Madrid wadda ta buga karawar ba tare da Cristiano Ronaldo ba, ta ci kwallayenta uku ta hannun Alvaro Morata da Mariano Diaz da kuma Sergio Ramos.

Ita kuwa Deportivo ta ci kwallayenta biyu ne ta hannun Joselu.

Da wannan sakamakon Real Madrid wadda rabon da ta lashe kofin La Liga tun a shekarar 2012 ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin gasar bana da maki 37.

Haka kuma ta goge tarihin lashe wasanni 34 a jere da ta yi ba a doke ta ba, wanda ta kafa a shekarar 1988-89 a karkashin kociya Leo Beenhakkeer.

Cikin wasanni 35 da Madrid din ta yi a jere ba a samu nasara a kanta ba, ta ci guda 26 ta kuma yi canjaras a fafatawa tara, ta zura kwallaye 98 a raga aka zura mata 34.