Dambe: Dan Aliyu da Aljanin Garkuwan Mai Caji sun yi canjaras

Damben gargajiya
Bayanan hoto,

Damben da aka tashi canjaras a ranar Lahadi a gidan damben Bambarewa

Kimanin dambe 11 aka yi a gidan damben gargajiya na Bambarewa da ke Marabar Yanya da ke jihar Nasarawa a ranar Lahadi da safe.

Ciki har da wasan da aka yi canjaras tsakanin Dan Aliyu Langa-Langa daga Arewa da Aljanin Garkuwan Mai Caji daga Kudu.

Sai dai kuma wasan da aka fara yin kisa shi ne wanda Shagon Casiyo daga Kudu ya buge Bahagon Dan Aliyu daga Arewa a turmi na biyu da wanda Habu Cingam daga Kudu ya doke Shagon Dan Aliyu daga Arewa a turmin farko.

Haka shi ma Shagon Musbahu daga Arewa ya doke Shagon Mari daga Kudu a turmin farko.

Shagon Amadi ne alkalin wasa, yayin da Makada sun hada da Habu na Habu da Rabiu Ashafa.

Ga wasannin da aka tashi babu kisa a gidan damben Bambarewa da ke Marabar Yanya:

Dan Shagon Dage daga Kudu da Bahagon Dan Aliyu daga Arewa.

Shagon Na Balbali daga Kudu da Shagon Aliyu daga Arewa.

Shagon Gidiwe daga Arewa da Shagon Habu Cingam daga Kudu.

Aljanin Shagon Alabo daga Kudu da Tulin Shagon Tuwo daga Arewa.

Dogo Shagon Lawwali daga Arewa da Shagon Kato Mai Karfi daga Kudu.

Autan Bahagon Sani Mai Maciji daga Kudu da Shagon Mai Kilishi daga Arewa.

Shagon Inda daga Arewa da Garkuwan Kugiya daga Kudu.