Premier: Chelsea ta koma ta daya

Diego Costa na zura kwallo a ragar Ben Foster.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Diego Costa ya zura kwallo a raga a hari shida da ya kai a cikin tara a gasar Premier

Chelsea ta koma saman tebur a Premier, kuma yanzu ta yi nasara sau tara a jere kenan a wasan da Diego Costa ya ci West Brom 1-0.

Dan wasan gaban na Spain ya yi amfani da damar da ya samu ne daga kuskuren da Gareth McAuley ya yi ne a minti na 76 ya jefa kwallo a ragar Ben Foster.

Kwallon ita ce ta 12 da Costa mai shekara 28 ya ci a gasar bana, wadda ta sa ya zo daidai da yawan kwallon da ya ci a bara.

West Brom ta dage kamar za ta ramar kwallon bayan da ta hana Chelsea sakat, in ban da harin da suka kai wanda David Luiz ya yi bugun tazara kawai.

Chelsean ta kuma samu wata damar inda ta kusa ci lokacin da N'Golo Kante ya kwarari wata kwallo da ta taba Pedro ta kauce

Da wannan nasara Chelsea, ta wuce Arsenal da maki uku yayin da West Bron din ta tsaya a matsayi na tara.

Rabon da West Brom ta ci Chelsea a Stamford Bridge a gasar lig tun watan Satumba na 1978.

Wasannin kungiyoyin biyu na gaba:

Chelsea za ta je gidan ta karshe a tebur Sunderland ranar Laraba (19:45 GMT) kafin ta yi wasan hamayya na Landan a gidan Crystal Palaceranar Asabar da karfe 12:30 GMT

West Brom kuwa za ta karbi bakuncin Swansea ranar Laraba (20:00 GMT) sannan kuma ta kara yin wani wasan a gida da Manchester United ranar Asabar da karfe 17:30 GMT.