Man Untd ta doke Tottenham 1-0

Henrikh Mkhitaryan ya zama dan Armenia na farko da ya ci kwallo a Premier, wanda hakan ya kawo 'yan kasashe 96 da suka ci kwallo a lig din a tarihi

Henrikh Mkhitaryan yana cin Tottenham

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Henrikh Mkhitaryan ya zama dan Armenia na farko da ya ci kwallo a Premier, wanda hakan ya kawo 'yan kasashe 96 da suka ci kwallo a lig din a tarihi

Kwallon da Henrikh Mkhitaryan ya fara ci a Premier League ta ba wa Manchester United damar nasara a kan Tottenham da suke hamayyar matsayi na hudu a tebur.

United, wadda har yanzu take maki shida a bayan Manchester City, ta hudu a kan tebur, ta samu kwallonta ne lokacin da Mkhitaryan ya yi amfani da kwallon da Ander Herrera ya zura masa, inda bai yi wata-wata ba ya shekata a raga a minti na 29.

Victor Wanyama ya kusa ya rama da wata kwallo da ya kai hari da ka daga tazarar yadi shida a harabar ragar Man United.

Duk ya cewa bakin, Tottenham sun rike kwallo sosai a wasan amma kuma ba su kai hare-hare masu kyau da yawa ba.

Paul Pogba ya kusa kara ta biyu da bugun tazara da ya dauka, inda kwallon ta bugi sandar raga, amma duk da haka nasarar ta kawo karshen wasanni uku da United ke yi ba tare da nasara ba.

Wasan ya kare ba tare da Mkhitaryan, ba wanda aka yi waje da shi saboda raunin da ya ji a idon kafa a minti goman karshe na wasan a Old Trafford.

Tottenham ta kuskure damar maye gurbin Man City a matsayi na hudu a tebur, abin da ya sa yanzu ta ci gaba da zama ta biyar, da maki uku a gaban Man United.