Southampton ta doke Middlesbrough 1-0

Cin da Sofiane Boufal ya yi wa Middlesbrough

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kwallon daya da Sofiane Boufal ya ci wa Southampton a baya ita ce wadda ta suka doke Sunderland 1-0 a gasar kofin Lig a watan Oktoba

Sofiane Boufal ya ci kwallonsa ta farko a gasar Premier, a wasan da Southampton ta doke Middlesbrough da ci daya ba ko daya.

Boufal wanda Southampton ta sayo shi daga Lille a watan Agusta kan kudin da ba ta taba kashewa ba wajen sayen dan wasa, har fan miliyan 16 ya samu kwallon ne daga James Ward-Prowse kafin ya shekata ta a ragar golan Boro Victor Valdes, a minti na 53.

Viktor Fischer ya samu babbar damar da bakin ya kamata su rama kwallon, amma sai Jose Fonte ya tare kwallon a bakin raga, bayan da Fischer ya kwararata

Nasarar ta kai Southampton matsayi na goma a tebur, yayin da Middlesbrough take ta 16, maki uku kawai a saman matakin faduwa daga gasar ta Premier.

Tarihi tsakanin kungiyoyin biyu;

Kwallon da Boufal ya ci ita ce ta 500 da Southampton ke ci a gidanta a gasar Premier, inda ta ci 256 a filin wasansu na da The Dell da kuma 244 da ta ci a St Mary.

Southampton ba ta taba cin Middlesbrough a gasar Premier a gida ba tun lokacin da ta ci ta 4-0 a watan Satumba na 1996

Wannan shi ne wasan Premier na farko tsakanin kungiyoyin biyu tun watan Maris na 2005, lokacin da Southampton ta yi nasara 3-1 a filin Middlesbrough, Riverside Stadium

Rashin nasarar shi ne na biyu na Middlesbrough a bana, kodayake sun yi canjaras a wasanninsu biyar daga cikin takwas a waje.

Wasannin kungiyoyin na Premier gaba;

Dukkanin kungiyoyin biyu za su yi wasan Premier ranar Laraba, inda Middlesbrough a gidanta za ta hadu da Liverpool (19:45 GMT), yayin da Southamptonza ta je gidan Stoke City (20:00 GMT).