Liverpool ta tsira a hannun West Ham 2-2

Loris Karius ya kasa tare kwallon Dimitri Payet

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wannan shi ne karo na uku da Dimitri Payet yake cin kwallo kai tsaye da bugun tazara a gasar Premier League

Kwallayen da Dimitri Payet da Michail Antonio suka ci sun kara fito da raunin bayan Liverpool a fili, a wasan da suka tashi canjaras 2-2 da West Ham, wadda ta fito daga rukunin faduwa daga Premier, a Anfield

Bayan da Bournemouth ta zura mata kwallaye hudu a karshen makon da ya wuce, Liverpool ta yi sake 'yan wasan biyu suka jefa kwallo biyu a ragarta a zagayen farko na wasan, yayin da take ba wa Chelsea da Arsenal dama suke kara kankane teburin gasar ta Premier.

Adam Lallana ya fara ci wa Liverpool kwallo a minti biyar da fara wasa, amma kuma sai bakin suka rama ta hannun Payet a minti na 27 da bugun tazara wanda mai tsaron raga Loris Karius na Liverpool ya yi sake kwallon ta wuce.

Can kuma a minti na 39 sai Antonio ya sake daga ragar Liverpool, har aka tafi hutun rabin lokaci 2-1.

Bayan an dawo daga hutu ne sai Divock Origi, ya farke wa masu masaukin bakin Liverpool, wasa ya zama 2-2 kamar yadda aka tashi, wanda hakan ya sa West Ham ta samu maki dayan da ya sa ta fito daga rukunin faduwa daga gasar ta Premier, ta zama ta 17.