Boksin: Joshua zai gwabza da Klitschko

Anthony Joshua da Wladimir Klitschko

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Joshua mai shekara 27, ya lashi takobin doke Klitschko mai shekara 41 a watan Afrilu

An yi hasashen damben boksin da za a gwamza tsakanin Anthony Joshua da Wladimir Klitschko a filin Wembley ranar 29 ga watan Afrilu zai iya tara 'yan kallon da aka taba tarawa a tarihin wasan a Birtaniya.

Bayan da Joshua ya doke Eric Molina ne ranar Asabara aka sanar cewa abokin karawarsa ta gaba shi ne tsohon zakaran damben ajin masu nauyi (heavyweight) Klitschko.

A tarihin damben boksin ba a taba tara 'yan kallo 90,000 da aka samu a karawar ajin kananan masu nauyi ba (light-heavyweights) na Len Harvey da Jock McAvoy a filin wasa na White City Stadium a 1939.

Jagoran hada damben Eddie Hearn ya ce: "ba shakka 'yan kallo dubu 80 ne za su halarta amma za mu nemi izinin karawa zuwa dubu 90.''

Ana kuma sa ran damben boksin din na Joshua da Klitschko zai iya zarta tarihin mutum miliyan 1.2 da suka kalli damben Floyd Mayweather da Ricky Hatton a talabijin a Birtaniya a 2007.

Hearn ya ce ana sa ran za su yi damben ne domin cin kambun duniya na WBA da IBF da kuma na Ring Magazine.

'Yan damben biyu dai zakarun Olympic ne a lokaci daban-daban, wadanda yanzu suka kai matsayin ajin masu nauyi na kwararru.

Joshua yana da tarihin kisan abokan karawa da dukan kwab-daya har 18 daga damben da ya yi tun lokacin da ya zama kwararre a 2013.

Shi kuwa Klitschko wanda ya zama kwararre a 1996 yayi nasara sau 64, inda 53 daga ciki ya yi ne ta hanyar dukan kwab-daya, an kuma yi galaba a kansa sau hudu.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Fury ya yi nasara a kan Klitschko da makin alkalan wasa a shekarar da ta wuce

Klitschko, dan kasar Ukrain, wanda ya cika shekara 41 a watan Maris, ya kai shekara 11 ba a doke shi ba, kafin Tyson Fury dan Manchester ya yi nasara a kansa a birnin Dusseldorf na Jamus a watan Nuwamba.

Sau biyu ana shirya sake haduwarsa amma damben bai tabbata ba, kafin daga baya Fury ya ajiye kambunan biyu na WBA da na WBObayan da aka gano yana amfani da kwayoyi, kuma ya bayyana cewa yana fama da larurar kwakwalwa hankali.

An kuma karbe kambun IBF daga Fury a watan Disamba na bara bayan da ya ki yarda ya gwabza da wanda hukumar kambun na IBF ta tsara ya kara da shi.

Daga nan kuma dan damben boksin na Amurka Charles Martin ya ci kambun wanda ba ya hannun kowa, kafin kuma Joshua ya kwabde shi a turmi biyu a watan Afrilu, ya kuma doke Dominic Breazeale a turmi na 7 a watan Yuni.

Joshua mai shekara 27, ya lashi takobin doke Klitschko a karawar tasu.