Luwadi: An dakatar da tsohon mataimakin kocin Chelsea

Dario Gradi

Dario Gradi

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Dario Gradi shi ne kocin Crewe daga 1983 zuwa 2007

An dakatar da darektan kungiyar Crewe Alexandra Dario Gradi har sai hukumar kwallon kafa ta Ingila ta kammala binciken da ya hada da zargin cewa ya taba neman sasantawa kan lalata da wani matashin dan wasan Chelsea.

Wani tsohon matashin dan wasan Chelsea inda a shekaru 1970 Gradi yake aiki a matsayin mataimakin koci, ya ce Eddie Heath, babban mai nemo wa kungiyar matasan 'yan wasa ya yi lalata da shi lokacin yana shekara 5, kuma Gradi ya shiga maganar domin sasantawa da shi da iyayensa.

Gradi, mai shekara 75, ya musanta yin wani abu da ya saba doka, kuma ya ce zai taimaka wa hukumar ta FA a binciken da take yi.

Shi dai Heath, wanda tuni ya mutu, mutane da dama sun zarge shi da lalata da su a shekarun 1970 da 1980.

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Gradi ya yi kocin Crystal Palace a 1981

BBC ta fahimci cewa FA, a matsayin binciken da take yi na luwadi da yaran 'yan wasan kwallon kafa, za ta yi wa Gradi tambayoyi bayan da jaridar Independent ta ruwaito cewa, a 1974, ya je ya gana da iyayen wani matashin dan wasan Chelsea a game da cin zarafinsa ta lalata da shi.

Tsohon matashin dan wasan wanda ba a bayyana sunansa ba saboda dalilai na shari'a, ya gaya wa jaridar cewa Gradi ya ziyarci iyayensa da shi domin sasanta lamarin.