Messi ya gana da yaron da ke matukar kaunarsa

Messi da Murtaza Ahmadi a Doha

Asalin hoton, SUPREME COMMITTEE

Bayanan hoto,

Messi tare da Murtaza Ahmadi, wanda ya yi rigar dan wasan ta leda, kuma hotonsa ya karade duniya

Wani yaro dan Afganistan wanda hotonsa ya karade duniya ta intnet bayan da ya sanya wata rigar wasa irinta Messi mai lamba goma, wadda ya yi da jakar leda ya gana da gwarzon nasa, Messin a zahiri.

A watan Janairu ne na shekarar da ta wuce hoton Murtaza Ahmadi dan shekara shida, sanye da rigar wasan da ya yi da leda mai zane-zanen shudi da fari da sunan Messi da kuma lamba 10 a jiki, ya yi ta yawo a intanet a duniya.

Hakan ya sa har Messin wanda ya ga hoton ya aiko wa yaron rigar ta gaske wadda ya yi mata rubutu da sanya hannunsa a jiki.

Bayan wannan lokaci, a yanzu Messin ya gana da yaron gaba da gaba a Doha, kamar yadda kwamitin shirya gasar cin kofin duniya ta 2022 da za a yi a Qatar ya bayyana.

Barcelona ta je Qatar ne domin wasan sada zumunta da kungiyar Al Ahli ranar Talata, kuma a lokacin wasan ne Ahmadi zai shigo fili tare da gwanin nasa, Messi.

A ranar Talata ne babban kwamitin shirya gasar ta cin kofin duniya da za a yi a Qatar din, ya sanya hoton Messi yana dauke da yaron, a shafin Tweeter, yana cewa: ''Ga hoton da duniya take son gani, yaro dan shekara 6 da ya ke da burin haduwa da gwaninsa Messi, a karshe burinsa ya cika."

A watan Mayu ne Ahmadi, wanda ya fito daga gundumar Jaghori, a gabashin lardin Ghazni na Afghanistan, suka yi gudun hijira daga kasar zuwa Pakistan.

Asalin hoton, TWITTER/JOYNAWS

Bayanan hoto,

Hoton Murtaza sanye da rigar ledar- abin da ya sa aka shiga neman mai kaunar Messin ta intanet

An gano Murtaza ne a hoton bayan da kawunsa, Azim Ahmadi, wani dan Afghanistan da ke zaune a Australia, ya hada shafin BBC na intanet da dan uwansa, wato mahaifin yaron.