Toure ya amince da laifin tuki cikin maye

Yaya Toure

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yaya Toure ya ce kowa ya san shi Musulmi ne, ba ya shan giya, amma ya amince da hukuncin

Dan wasan tsakiya na Manchester City Yaya Toure, ya amince da aikata laifin tukin mota cikin maye, amma kuma ya ce ba da niyya ya sha giya ba.

Dan wasan na Ivory Coast, mai shekara 33, ya yarda cewa ya zarta yawan giyar da ya kamata a ce wanda zai tuka mota ya sha, kuma bai kalubalanci tuhumar da aka yi masa ba.

Kotun majistare ta Barkingside ta ci tararsa fan dubu 54, tare da hana shi tukin mota har tsawon wata 18.

A martanin da ya mayar game da lamarin Toure ya ce: "Abu ne da kowa ya sani cewa ni Musulmi ne, ba na shan giya. Kodayaushe ba na karbar giya.''

A watan da ya wuce ne aka kama Toure da laifin tuki cikin maye a Dagenham da ke gabashin Landan.

A ranar Litinin ne Toure ya amince da tuhumar, amma kuma bai bayyana a shafinsa na Facebook ba yadda aka yi har ya sha barasar ba.

A wata sanarwa da ya fitar Touren ya kara da cewa: "Tuki cikin maye babban laifi ne, kuma duk da cewa ban sha giya da niyya ba, na amince da hukuncin, kuma ina ba da hakuri a kan lamarin."