Ingila na neman kocin 'yan kasa da 21

Gareth Southgate

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Southgate ne kocin 'yan kasa da shekara 21 kafin ya samu cigaba zuwa babbar tawagar kasar

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, tana neman sabon kocin tawagar kwallon kasar ta 'yan kasa da shekara 21 wanda zai maye gurbin Gareth Southgate, da sharadin kai ta ga nasarar cin kofin duniya na 2022.

An dai samu gurbin ne byan da aka daga likkafar Gareth Southgate ya zama kocin babbar kungiyar kasar a kan wata yarjejeniya ta shekara hudu.

An dai ba wa mai horar da tawagar 'yan kwallon kasar ta 'yan kasa da shekara 20 Aidy Boothroyd rikon mukamin na wucin-gadi, inda ya maye gurbin Southgate.

A sanarwar da hukumar ta FA, ta fitar ta tallata aikin, ta ce, tana neman kocin ne, da burin daukar kofin duniya na a 2022 da kuma dorewar nasara bayan gasar.

Tawagar ta Ingila ta 'yan kasa da shekara 21 ta samu tikitin zuwa gasar cin kofin kasashen Turai da za a yi a bazara mai zuwa a Poland duk da wasa daya da ya rage musu.