Guardiola: Ina bukatar lokaci kafin na gina Man City

Kocin Manchester City Pep Guardiola

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Guardioa ya ce: 'Hatta taurarona Sir Alex Ferguson sai bayan shekara 11 ya fara cin kofi''

Kocin Manchester City Pep Guardiola ya ce yana bukatar karin lokaci kafin ya gina kungiyar ta yadda za ta rika cin kofi.

Kashin da Leicester City ta ba su ranar Asabar, shi ne karo na biyu a jere da aka doke Cityn a gasar Premier bana - kuma karo na farko da suka yi rashin nasara a jere a gasar Premier a karkashin Guardiola.

City na bayan Chelsea ta daya a tebur da maki bakwai tsakaninsu , kuma wasa hudu kawai suka ci a wasansu 15 a gasa daban-daban.

Da aka tambayi , Guardiola kan rashin tabuka abin-a-zo-a-ganida kungiyar ke yi, ko hakan na nuna cewa ya gaza, sai ya ce, a ba shi lokaci.

Idan abin da ya faru a watan da ya wuce aka duba ya ce to lalle kam ya gaza.

City, wadda za ta karbi bakuncin Watford ranar Larabar nan, ba ta ci wani wasa a gida ba tun lokacin da ta casa Barcelona 3-1 a gasr cin kofin Zakarun Turai ranar 1 ga watan Nuwamba.

Guardiola, wanda ya karbi aikin kocin Manchester City a bazarar da ta wuce, ya ce tsohon kocin Manchester United Sir Alex Ferguson babban misali ne na dalilin da kungiyar tasa za ta kara hakuri.

Sir Alex Ferguson, wanda ya zama kocin United a watan Nuwamba na1986, ya ci kofin premier 13 Premier League titles as United manager, amma kuma sai a 1993 ya fara daukar kofin.

Guardiola, mai shekara 45, wanda ya duki kofi 21 a lokacin yana kocin Barcelona da Bayern Munich, ya kara da cewa

"Sir Alex Ferguson, wanda shi ne taurarona, bai ci kofi ko da daya ba a Man United sai bayan shekara 11, kuma Liverpool ba ta dauka ba tsawon shekara 25.