Premier: Everton ta yi wa Arsenal kancal da ci 2-1

Everton da Arsenal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Everton ta kawo karshen wasanninta biyar ba nasara, wanda rabonta da cin wasa tun Oktoba

Everton ta yi wa Arsenal wadda ke fatan karbar jagorancin Premier, kancal bayan da ta doke ta da 2-1 a wasansu na mako na 16, inda su ma zakarun gasar Leicester suka sha kashi 1-0 a gidan Bournemouth.

Arsenal din ta ci gaba da kasancewa ta biyu da maki uku tsakaninta da ta daya Chelsea mai maki 37, sai dai Chelsean ba ta yi wasanta na makon na 16 ba tukuna, sai ranar Laraba, inda za ta je gidan Sunderland.

Sanchez ne ya fara ci wa Arsenal kwallo a minti na 20, to amma kuma sai Gunners din suka yi sake Colemann ya farke a minti na 44 ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Can kuma bayan wasa ya mika, ya kama hanyar karewa sai kwatsam a minti na 84, Williams ya yi wa Arsenal mai gaba daya ya ci su kwallo ta biyu.

Nasarar ta ba wa Everton damar dagawa zuwa mataki na bakwai da maki 23, a wasanni 16.

Bournemouth da Leicester:

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Marc Pugh ya kwarara kwallon tsakanin 'yan wasan Leicester

A daya wasan da aka yi tsakanin Bournemouth da Leicester wadda ke rike da kofin na Premier, zakarun sun yi rashin nasara da ci 1-0.

Wannan ya sa Bournemouth ta zama ta takwas a tebur da maki 21, yayin da Leicester din take mataki na 14 da maki 16.

Ga wasannin da za a cigaba da su a ranar Laraba, na gasar ta Premier na mako na 16:

Middlesbrough da Liverpool

Sunderland da Chelsea

West Ham da Burnley

Crystal Palace da Manchester United

West Bromwich da Swansea City

Manchester City da Watford

Stoke City da Southampton

Tottenham da Hull City