Mourinho na bukatar karin 'yan wasa

Jose Mourinho kocin Manchester United

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A bazara ne Mourinho ya kulla yarjejeniyar shekara uku ta zama kocin Man United

Jose Mourinho yana bukatar akalla lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa biyu kafin ya kusa hada tawagar 'yan wasan da yake bukata in ji manyan shugabannin Man United.

Wata bakwai bayan da Mourinho ya gaji Louis van Gaal, United tana matsayi na shida a teburin Premier, maki 13 a bayan Chelsea ta daya.

Kuma maki shida tsakaninta da matakin kungiyoyi hudu na gaba-gaba a gasar da ke samun gurbin zuwa gasar kofin Zakarun Turai.

Da yake magana kan shirin tunkarar wasansu a gidan Crystal Palace na ranar Larabar nan (20:00 GMT), Mourinhoya ce yana son barin 'yan wasansa yadda suke a yanzu har zuwa karshen kakar bana.

Sai dai kuma wasu kafafe sun gaya wa BBC cewa kocin yana son yin wasu sauye-sauye a tawagar.

United ta kashe fan miliyan 480 wajen sayo 'yan wasa tun lokacin da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya a matsayin koci a 2013 bayan shekara 26.

Kungiyar ta kashe kudin da ba ta taba kashewa ba a sayen dan wasa, lokacin da ta sayo Juan Mata daga Chelsea a watan Janairu na 2014 a kan fan miliyan 37.1.

Sannan kuma sun kashe kudin da wata kungiya ba ta taba kashewa ba a Birtaniya wajen sayen dan wasan gefe na Real Madrid Angel di Maria a cikin shekarar ta 2014, a kan fan miliyan 59.7.

A watan Agusta na wannan shekara ta 2016, kungiyar ta kuma ba wa Mourinho kudin da ba a taba kashewa ba wajen sayen dan wasa, inda ya sayo Paul Pogba kan fan miliyan 89 daga Juventus.

BBC ta fahimci cewa shi kansa Mourinho ya yadda cewa ba abu ne mai sauki ba sayo manyan 'yan wasa masu tsada, amma kuma ana ganin ya dauki hakan a matsayin wani abu wanda babban mataimakin shugabn kungiyar Ed Woodward zai shawo kansa.

Wadanda ake ganin zai rabu da su:

Memphis Depay da Morgan Schneiderlin da Sam Johnstone (zai bayar aro) da Ashley Young da Bastian Schweinsteiger

Wadanda ake ganin zai bari:

David de Gea da Michael Carrick da Ander Herrera da Henrikh Mkhitaryan da Zlatan Ibrahimovic da Wayne Rooney da Anthony Martial da Marcus Rashford da Jesse Lingard da Juan Mata da

Paul Pogba da Antonio Valencia da Timothy Fosu-Mensah da Chris Smalling da Phil Jones da Eric Bailly da Sergio Romero

Wadanda ake ganin babu tabbas kan zamansu:

Marcos Rojo da Matteo Darmian da Daley Blind da Luke Shaw da Marouane Fellaini