Oscar zai bar Chelsea, Arsenal na fargaba kan Sanchez

Oscar

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

A watan Janairu dan wasan na Brazil zai koma China

Chelsea ta amince da tayin fan miliyan 60 da kungiyar Shanghai SIPG ta China wadda tsohon kocin Chelsean Andre Villas-Boas ke jagoranta ta yi a kan dan wasanta na tsakiya Oscar.

Jaridar Daily Telegraph ta ruwaito cewa a watan Janairu ne dan wasan na Brazil mai shekara 25 zai koma kungiyar ta China.

Kocin Chelsea Antonio Conte ya ce ba zai ba da tabbacin cewa dan wasan tsakiya Cesc Fabregas, mai shekara 29, zai ci gaba da zama a kungiyar ba bayan rufe kasuwar saye da sayar da 'yan wasa mai zuwa in ji London Evening Standard.

Arsenal na dab da kammala yarjejeniyar ba wa Olivier Giroud, mai shekara 30, sabon kwantiragi, da shi da dan wasanta na tsakiya Francis Coquelin, mai shekara 25.

Yayin da shi kuwa Mesut Ozil, mai shekara 28, Arsenal din ke ganin zai iya amincewa da wani sabon kwantiragin shekara biyar,.

Sai dai kuma Gunners din na da fargaba a kan Alexis Sanchez mai shekara 27 kan ko zai cigaba da zama, a kungiyar kamar yadda Daily Mail ta labarto.

Chelsea da Bayern Munich na daga kungiyoyi da dama da suke harin dan wasan tsakiya na Tottenham Eric Dier, musamman yadda dan wasan mai shekara 22, ba ya jin dadin yadda yake zaman benci a White Hart Lane, in ji Times.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Manchester United kuwa tana dab da kammala cinikin dan wasan Ajax na gaba Daishawn Redan, mai shekara 15, wanda ya yi wa tawagar Holland ta 'yan kasa da shekara 17 in ji Squawka.

Dan wasan Manchester United Memphis Depay, mai shekara 22, da dan wasansu na tsakiya Morgan Schneiderlin, mai shekara 27, za su iya barin United din su koma Everton a watan Janairu kamar yadda Daily Mail ta ruwaito.

Kocin Man United din Jose Mourinho yana fargaba kan yadda dan wasansa Marcus Rashford ke fama da irin yadda ake yayata gwanintarsa.

Kuma kocin ya yi matukar fushi kan yadda har sau biyu a wasansu da Tottenham ranar Lahadi, aka wuce da kwallo ta tsakankanin kafar matashin dan wasan mai shekara 19, in ji Sun.

Haka kuma jaridar Sun din ta ruwaito cewa Chelsea da Barcelona da Bayern Munich suna zawarcin dan wasan tsakiya na Rangers Billy Gilmour, dan shekara 15.

Leicester City na shirin daukar dan wasan tsakiya na kungiyar Genk, dan Najeriya Wilfred Ndidi a kan kusan fan miliyan 15 idan aka kammala gwajin lafiyar dan wasan mai shekara 19, in ji Guardian.

Ita kuwa Borussia Dortmund ta gaya wa Liverpool ne kada ta ma nuna sha'awarta kan matashin dan wasanta, Ba'amurke Christian Pulisic mai shekara 18, a watan Janairu, lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa, kamar yadda jaridar Liverpool ta ruwaito daga Bild.

Tsohon dan wasan Arsenal da Jamus Jens Lehmann yagaya wa kocin Liverpool Jurgen Klopp kada ya ajiye mai tsaron ragarsa Loris Karius, mai shekara 23 kamar yadda Talksport ta ruwaito

Wadannan dai labarai ne da wasu jaridu da kafafen yada labarai na Burtaniya da Turai suka ruwaito game da kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa da ke tafe