An fara amfani da bidiyo a gasar Fifa

Amfani da hoton bidiyo a wasan Fifa a karon farko

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alkalin wasa Viktor Kassai na tantance hoton bidiyo kafin daga bisani ya bayar da fanareti

Kashima Antlers ta Japan ta zama ta farko da ta ci gajiyar tsarin amfani da hoton bidiyo a gasar, Fifa, inda ta samu bugun fanareti ta ci 3-0 a wasan kusa da na karshe na cin kofin duniya na kungiyoyi.

Alkalin wasa Viktor Kassai ya tsayar da wasan ne wanda ake yi a Japan, bayan da mataimakinsa mai lura da hoton bidiyon wasan ya ankarar da shi kan wani laifi da aka yi, inda ya bayar da fanareti bayan ya kalli bidiyon.

Kungiyar Kashima ta doke Atletico Nacional ta Colombia, wanda hakan ya sa ta zama kungiya ta farko daga Asia da ta yi nasarar zuwa wasan karshe na gasar.

A ranar Lahadi ne Zakarun na Asia za su kara a wasan karshe da Zakarun Turai Real Madrid ko Zakarun Amurka ta Arewa Club America.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alkalin wasa Viktor Kassai ya bayar da fanareti

Su kuwa zakarun Afirka, Mamelodi Sundowns na Afirka ta Kudu, an yi waje da su ne daga gasar a jiya Laraba, bayan an sake doke su a karo na biyu a wasannin da suka yi a gasar.

A wannan karon kungiyar Jeonbuk Motors ce ta Koriya ta Kudu ta casa su da ci 4-1 a wasan neman matsayi na biyar.

Kungiyoyin da suka yi nasarar zama Zakarun nahiyoyi shida ne na Fifa, ke shiga gasar ta cin kofin duniya na kungiyoyi.