An dakatar da gasar kwallon kafa ta Congo saboda fargaba

'Yan wasan tawagar kasar DRC

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan tawagar kasar Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo

An dakatar da babbar gasar lig ta kwallon kafa ta Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo saboda fargabar barkewar rikicin siyasa.

An dauki matakin ne saboda ana ganin idan rikici ya barke a yanayin da ake ciki zai iya watsuwa har zuwa wuraren kallon wasan kwallon kafa a fadin kasar.

Ana dai fargaba ne saboda wa'adin mulkin shugaba Kabila zai kare, kuma an jinkirta zabukan kasar, a kan hakan ake ganin zaman dar-dar zai iya bazuwa har filayen wasa, wanda rikici zai iya tashi daga nan.