Damben Boksin: Amir Khan da Kell Brook na shirin gwabzawa

Karon Saul 'Canelo' Alvarez da Amir Khan

Asalin hoton, JOHN GURZINSKI

Bayanan hoto,

Saul 'Canelo' Alvarez ne ya doke Amir Khan a dambensa na karshe

'Yan damben boksin Kell Brook da Amir Khan dukkaninsu 'yan Birtaniya suna shirin gwabzawa a watan Mayu na 2017, kamar yadda wakilin Brook, Eddie Hearn ya tabbatar.

A farkon wannan shekaran ne aka ji Amir Khan mai shekara 30 yana cewa Sheffield Brook shi ma mai shekara 30 ba tsaransa ba ne a dambe.

Amma kuma a ranar Larabar da ta gabata, sai aka ga Khan a shafukan sada da zumunta da muhawara, yana nuna cewa shi ne dan boksin na gaba da zai gwaggwabje fuskar Brook.

Sai shi ma Brooks ya mayar masa da martani da cewa yana son ya sake mayar da Amir Khan din barci.