Liverpool ta ba wa Balotelli kudi don kada ya tofar da yawu

Mario Balotelli ya rufe bakinsa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ko Balotelli yana tofar da yawun ne a jikinsa a nan?

Ko ka san cewa a kwantiragin 'yan wasa wani lokaci akwai wasu yarejeniyoyi masu ban dariya ko ban haushi? Daya daga cikinsu ita ce idan Balotelli ya tofar da yawu sau uku a fili, za a ci tararsa fan miliyan daya, idan kuma ya kiyaye za a ba shi kudin kyauta.

Kungiyar Liverpool ce ta gindaya wa tsohon dan wasanta, dan Italiya, Mario Balotelli, lokacin da za ta saye shi daga AC Milan, wasu sharuddan da suka hada da wannan.

Sharadin da aka sanya masa shi ne kasancewar dan wasa ne mai yawan tofar da yawu a fili, ko dai bisa yanayin dabia'rsa ko kuma domin nuna kyama ga wani abu da aka yi masa, da kuma fushi, domin shi mutum ne da ake ganin ba ya barin ta-kwana, kada ya tofar da yawu sau uku a fili, ko ya yi fada ko zagi, da za su kai ga korarsa a fili sau uku.

Ana son ya kiyaye da hakan tsawon kowace shekara ta kwantiragin nasa, wanda idan bai kiyaye da hakan ba, har ya aikata abubuwan, kungiyar za ta ci tararsa fan miliyan daya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ko a nan ma Balotelli yana kokarin kiyayewa da sharadin tofar da yawun ne?

Amma kuma idan har ya kiyaye, ko da sau biyu aka ba shi jan kati, na kora, bai kai sau uku ba, to Liverpool za ta ba shi kyautar wannan kudi fan miliyan daya.

A karshe Liverpool ta cika alkawarin, bai wa dan wasan wanda yake kungiyar Nice ta Faransa a yanzu, wannan lada na fan miliyan daya.

Wannan bayani dai yana kunshe ne a wasu takardu na sirri da aka yi satar fitar da su ga jaridar Sunday Times, wadanda suka shafi kwantiragin dan wasan da Liverpool.

Liverpool ta sayo Balotelli ne daga AC Milan a 2014 akan fan miliyan 16, a kwantiragin da ya tanadin sharadin na tabbatar da da'arsa a wasa.

Dan wasan mai shekara 26 wanda ake yi wa kallon mai wuyar sha'ani da kan jawo ce-ce-ku-ce, a yanzu ana ganin ya ba marada kunya yadda yake taka rawar-gani a Nice, abin da zai iya kai ta ga daukar kofin lig din Faransa a bana.

Haka shi ma tsohon dan wasan kwallon kafar Ingila Razor Ruddock, a farkon shekarun 1980 zuwa da 90, an yi masa sharadin yanke masa kashi 10 cikin dari na albashinsa na mako, idan ya kai nauyin kilogram 100.

Razor Ruddock ya yi kungiyoyi Liverpool da Tottenham da Southampton da kuma West Ham.